Tsadar rayuwa wata matsala ce da ke neman zame wa duniya wata babbar barazana. Inda ƙasashen duniya da dama ke cikin wannan matsala, sakamakon tashin farashin abubuwan amfani na yau-da-kullum. A baya-bayan nan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka irinsu Ghana da Nijar na fuskantar matsalar tsadar rayuwa. To sai dai matsalar ba ta tsaya ga nahiyar Afirka kaɗai ba, al'amari ne da ya shafi duniya baƙi-ɗaya. Shin me ke haifar da wannan matsala da tsadar rayuwa a faɗin duniya? 1-Tashin farashin makamashi da man fetur An samu ƙaruwar farashin man fetur tun bayan ɓarkewar annobar korona, inda buƙatar man fetur ɗin ta ƙaruwa a duniya sakamakon matakin kullen korona da ƙashen duniya da dama suka ɗauka. Wannan abu ya sa man fetur ɗin ya kai tsadar da bai taɓa kai wa ba cikin shekaru masu yawa. A yanzu dai ana sayar da gangar ɗanyen mai man fetur kan dala 79 zuwa sama a kasuwannin duniya. Hakan ya faru ne sakamakon yaƙin Ukraine da Rasha, Ita dai Rasha na cikin ƙasashen da suke da arzikin man f...
Masana tattalin arziki a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin kasar ke dauka da kyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo karshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da bude iyakoki domin shigowa da abinci cikin kasar ba. ‘Yan Najeriya, musanman talakawa na ci gaba da kukan tsada da hauhawar kayan masarufi a kasuwannin kasar. Biyo bayan zanga zangar lumana da wasu mata suka jagoranta a jihar Neja da kuma wasu daban da aka gudanar a jihohin Kano da Osun, ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, daukan matakan ba da umarnin fito da tan-tan na abinci da ke runbunan gwamnantin kasar, domin karya farashin kayan masarufi da ke neman ya gagari kundila. To sai dai kuma a cewar wani masanin harkar gona, Farfesa Abubakar Gudigi, na jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, ya ce da sake a wannan dabara ta gwamnati. Gudigi ya ce matakin gwamnati na karya farashi, ba shi zai kawar da yunwa ba, domin yanzu haka akwai wadanda ke sayen kayan abinci a kauyuka, domin sayarwa...