Ake ciki sannan dan kasuwa shi ma yana fuskantar koma-bayan ciniki saboda mutane na fama wajen samun kudin da za su shiga kasuwa.
Ya ce tsugunu ba ta kare ba a damar da gwamnati ta bayar na ba da dala ga duk mai son shigar da abinci daga wasu kasashen kasancewar dalar ta yi karanci a babban bankin Najeriya.
"Domin duk wanda zai siyo abinci a waje, ko dai ya canza naira zuwa dala, ko naira zuwa CFA, ko zuwa me ka canza naira, idan ka siyo abincin ba za ka sayar da shi a kan sauki ba." in ji Dr Kani.
Dr Muhammad Suleiman Kani ya ce matukar gwamnati na son kawo sauki toh kamata ya yi gwamnati ta haramta shigar da duk kayan da za a iya samu a Najeriya.
A cewarsa, idan gwamnati ta dauki wannan mataki, ya kamata ta hanzarta tayar da komadar kamfanoni da wutar lantarki domin su tsaya da kafafunsu.
Ya kuma yi kira ga shugaban kasa ya tashi tsaye wajen yin abin da ya dace domin fitar da Najeriya daga kangin da take ciki.
A cewar masanin, ya kamata gwamnati ta cika alkawuran da ta daukar wa jama'a bayan janye tallafin man fetur na kara albashi da inganta walwalar al'umma da tayar matatar mai ta Fatakwal.
A cewar kwararren kan samar da abinci, tsarin shigar da abinci daga wasu kasashen hanya ce mai kyau sai dai akwai bukatar gwamnati ta sa ido domin tabbatar da cewa tsarin ya tafi sumul kalau ga amfanin yan kasa.
Ya ce "dole hukumomin tsaro su sa ido saboda dabi'ar yan Najeriya, za a iya shigar da kayan abincin sai ka ga wasu tsirarun mutane sun debe abincin an sauya buhu, sun kai shi kasuwa ana kuma cinikinsa."
Ya kuma ce bai kamata gwamnati ta sake kuskuren bayar da abincin ta hannun gwamnoni ba, kasancewar irin wannan tsarin a baya, bai yi nasara ba.
Dr Kani ya ce a yi amfani da kasuwannin da ake da su da kuma cibiyoyin gwamnati na harkar abinci, sannan a yi tsarin a bude, "babu maganar gwamnoni ko yan majalisa."
Ya ce gwamnati ta aiwatar da abin da kanta sannan ta saka yan farar hula da za su sa ido kan yadda tsarin ke tafiya domin tabbatar da an yi shi bisa gaskiya.
Dr Muhammad Kani ya bayyana cewa tsarin na gwamnati zai iya shafar harkokin yan kasuwa inda ya ce a wasu kasashe kamar Amurka gwamnati tana siyan kayan abinci sai ta rage farashinsu a duk lokacin da aka gama harkokin noma.
Ya ce tsarin bai tsaya iya nan ba, Saudiyya ma tana aiwatar da irin tsarin.
"A Saudiyya, akwai lokacin da idan kaya suka yi yawa sai ta gayyato manoma, ta ce kada su yi noma," tana tambayar nawa ce ribarsu sai ta dauki ribar ta basu.
"Saboda idan ya yi yawa ya wuce hankali za a yi asara, za ku noma ba ku ci riba ba." kamar yadda ya ce.
A cewar masanin, daukan wannan tsarin zai kawo gasa kuma zai sa wadanda suke samar da abin na cikin gida suma su karyar da farashin kayansu.
Masanin ya ce rashin isassun rumbuna ka iya kawo tarnaki ga matakin shigo da kayan abincin saboda rashin tanadin wuraren da za a ajiye su wanda hakan zai iya jawo lalacewarsu.
Ya kuma a yanzu gwamnatin ba ta da kayan abincin a kasa, a yanzu ne za ta shigo da su kuma abin tambayar a cewarsa shi ne da wane kudi za ta siyo kayan?
Ya ce ma'ana dole sai gwamnati ta ciwo bashi domin sayo kayan abincin.
AMH Hausa