Skip to main content

Abubuwan da suka haifar wa duniya tsadar Rayuwa

Tsadar rayuwa wata matsala ce da ke neman zame wa duniya wata babbar barazana.

Inda ƙasashen duniya da dama ke cikin wannan matsala, sakamakon tashin farashin abubuwan amfani na yau-da-kullum.

A baya-bayan nan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka irinsu Ghana da Nijar na fuskantar matsalar tsadar rayuwa.

To sai dai matsalar ba ta tsaya ga nahiyar Afirka kaɗai ba, al'amari ne da ya shafi duniya baƙi-ɗaya.

Shin me ke haifar da wannan matsala da tsadar rayuwa a faɗin duniya?

1-Tashin farashin makamashi da man fetur

An samu ƙaruwar farashin man fetur tun bayan ɓarkewar annobar korona, inda buƙatar man fetur ɗin ta ƙaruwa a duniya sakamakon matakin kullen korona da ƙashen duniya da dama suka ɗauka.

Wannan abu ya sa man fetur ɗin ya kai tsadar da bai taɓa kai wa ba cikin shekaru masu yawa.

A yanzu dai ana sayar da gangar ɗanyen mai man fetur kan dala 79 zuwa sama a kasuwannin duniya.

Hakan ya faru ne sakamakon yaƙin Ukraine da Rasha, Ita dai Rasha na cikin ƙasashen da suke da arzikin man fertur da iskar gas.

Sakamakon yaƙin Ukraine ya sa ƙasar ta rage adadin man da ke fitarwa zuwa kasuwannin duniyar, sannan kuma takunkuman karya tattalin arziki da wasu ƙasashen duniya suyka sanya mata, ya sa sun dai sayen man ta.

Sannan matakan takunkuman sun sa Rashar ta daina sayar wa wasu ƙasashen Turai man fetur da kuma iskar gas.

Hakan ya sa wasu ƙasashen mayar da hankali zuwa wasu ƙasashen duniya domin sayen man fetur da gas ɗin da suke amfani da shi, hakan ne ya sa farashin man fetur ɗin da na iskar gas ya ƙaru a duniya.

2- Annobar korona

Annobar korona na daga cikin manyan abubuwa da suka haifar da ƙaruwar hauhawar farashi a faɗin duniya.

A lokacin annobar an dakatar da kusan duka zirga-zirgar mutane da kayyaki, lamarin da ya sa ƙasashen da suka dogara da da kayyakin da ake shigar musu, suka shiga halin matsi da tashin farashin kayyaki.

Kuma ko bayan wucewar wannan annoba har yanzu irin wadannan ƙasashe ba su kammala farfaɗowa daga cikin matsin da suka shiga a lokacin ganiyar annobar ba.

''Dokar kullen da ƙasashen duniya suka shiga ta taimak sosai wajen ƙara durƙusar da harkokin kasuwanci a faɗin duniya, kama daga harkokin jigilar jiragen sama da na ruwa, zuwa harkokin noma da sauran kayyakin masana'antu'', kamar yadda Dakta Yusha'u Aliyu wani mai sharhi kan tattalin arziki a Najeriya ya bayyana

3- Yaƙin Ukraine

Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a farkon shekarar 2022 ya sake dagula al'amara ta fuskar hauhawar farsahin kayayyaki.

Rasha da Ukraien sun kasance manyan ƙasashe biyu da ke fitar da alakama da sauran nau'in hatsi zuwa kasuwannin duniya.

Barkewar yaƙi tsakanin ƙasashen biyu ya kawo cikas ga fitar da abinci da ƙasashen biyu ke yi zuwa ƙasashen Duniya, musamman ƙasashen Afirka waɗanda suka dogara sosai ga manyan ƙasashen biyu wajen shigar da alkama da sauran nau'o'in hatsi zuwa ƙasashensu.

''Yaƙin Ukraine da Rasha na daga cikin manyan batutuwan da suka haddasa tashin farashin kayayyaki musamman na abinci a fadin duniya'', in Yusha'u Aliyu.

4- Hare-haren tekun Maliya

Bayan barkewar yaƙin ISra'ila da Hamas cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata, 'yan tawayen Houthi da ke Yemen sun riƙa kai hare-hare kan jiragen dakon kaya a tekun Maliya, da nufin hana duk wani jirgi da ke ɗauke da kaya zuwa Isra'ila a wani mataki na nuna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza.

Wannan abu ya sa 'yan tawayen sun riƙa kai hari kan kowane jirgi ma da suka yi zargin na Isra'ila ne ko yana kan hanyar zuwa Isra'ila a tekun.

Hakan ya sa jiragen ruwan sun riƙa yin dogon zagaye, don kauce wa hare-haren 'yan tawayen na Houthi a tekn na Maliya.

''Hakika hakan ya haifar da ƙaruwar farashi a duniya, sakamakon dogon zagayen da jiragen dakon kayyaki ke yi'', kamar yadda Yusha'u Aliyu ya bayyana.

5- Sauyin yanayi
Dumamar yanayi a wasu sassan duniya na daga cikin abubuwan da suka sake ta'azzara hauhawar farshin kayayyaki a duniya.

a ƙasashe da dama damina na fuskantar cikas, lamarin da ke haifar da tasgaro kan abubuwan da aka shuka.

Alal misali a ƙasashen Somaliya da Habasha da wasu sassa na ƙasar Kenya, sai da aka shafe kusan shekara biyar ba tare yin girbi ba, sakamakon mummunan fari da suka fuskanta tsawon shekaru.

Don haka dole ne waɗannan ƙasashe su buƙaci shugar da abinci domin ciyar da al'ummar ƙasashensu.

Haka kuma a ƙasashe irin su Brazil da ke kan gaba a noman koffi a duniya, an samu matsalar damina sakamakon mummunan fari mafi muni da aka samu a shekarun baya a ƙasar.

Me ya sa matsalar ta fi ƙamari a ƙasashe irin Najeriya?

Matsalar tsadar rayuwa da ake fuskanta a Najeriya ta sha bamban da matsalolin da suka haifar da matsalar a wasu ƙasashen duniya.

A Najeriya akwai matsalolin da masana ke ganin su ne suka haifar da matsalar, waɗan da suka hadar da:

1- Matsalar rashin tsaro

Matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta sakamkon ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, kamar Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, da kuma 'yan fashin daji a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya sun tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu ba tare da nomawa ba.

Al'ummomin yankin arewacin Najeriya, sun dogara da noma ne wajen samun abin da za su ci.

To sai sakamakon ayyukan 'yan bindigar waɗannan ke sace mutane, musamman manoma, ko kashe su a gonakinsu.

A wasu yankunan kuma 'yan bindigar ne ke ƙwace gonakin, ko su hana mutane girbi bayan kammala noma, ko su ce sai manoman sun bya kudin haraj kafin su girbe amfanin gonarsu.

Wannan al'amari ya sa mutane da dama sun haƙra da noman, domin tsira da rayuwarsu, lamarin da ya taimaka matuƙa wajen ƙarancin abinci a jihohin arewacin ƙasar, da ma Najeriya baki-ɗaya.

''Idan aka samu rashin tsaro a inda gonaki suke, to ka ga babu dama mutanen da ke zuwa gonaki don noma su samu sukunin zuwa noma, to in kuwa ba su yi noma ba, dole farashi ya sauya a kasuwanni''.

2- Ambaliyar ruwa

Ambaliya ruwa na daga cikin matsalolin da ke haifar da ƙaruwar farshin kayyaki musamman na noma a Najeriya da ma kasashen Afirka sakamakon sauyin yanayi da duniya ke fama da shi.

''Yanayi ne da idan an shuka amfanin gona, sai ruwa ya zo ya tafi da shi, to ka ga an samu raguwarsa, don haka dole ne a samu tashin farashin kayan noma'', in ji masanin tattalin arzikin.

3- Tsadar kayan noma

Tashin farashin kayyakin noma kamar su taki da magungunan feshi sun ƙara ta'azzara tsadar kayan abinci a Najeriya.

Yusha'u Aliyu ya ce ''duk manomin da ya sayi kayan aikin noma da tsada to tabbas ba zai zo kasuwa ya sayar araha ba, saboda duk wanda ke noma, yana yi ne don riba, babau wanda yake yi don faɗuwa''.

Masanin tattalin arzikin ya ce ''idan aka samu ƙari a kayan zirga-zirga, to dole ne manoma su sauya farashin da suka saba sayar da kayyakinsu a baya''.

4- Rufe iyakokin Najeriya
Wani Abu da ya sake dagula hauhawar farashi da tsadar rayuwa aNAjeriya shi ne matakin ggwamnatin ƙasar na rufe kan iyakokin ƙasar don hana shigo da kayan abinci.

Mutane da dama a Najeriya sun dogara da abubuwan da ake shigo da su daga ƙasashen ƙetare, don haka matakin rufe iyakokin ya sake haifar da farashinna cikin gida, sakamakon ƙaruwar masu buƙatar kayyakin.

Masanin tattalin arzikin ya ce ''matsawar aka rufe iyakoki, kuma ba a samu abin da ake buƙata a cikin ƙasa ba, to dole ne a samu tashin farashin abin da ake da shi a cikin gida''.

5- Cire tallafin mai
Tallafin man fetur na daga cikin manyan abubuwan da suka hassada ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Cikin jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanar da matakin cire tallafin man fetur.

Matakin ya haifar da ƙaruwar farashin man feter din a fadin ƙasar, lamarin da ya shafi farashin sufurin kayayyaki da sauran abubuwa.

''Man fetur ɗinnan da shi ne ake amfani wajen jigilar sauran kayayyaki zuwa kasuwanni, don haka tashin farashin man fetur dole ne ya haddasa ƙaruwar farashin kayyaki'', in ji Yusha'u Aliyu.

6- Karyewar darajar kuɗin ƙasar

Karyewar darajar kuɗin Najeriya na daga cikin batutuwan da ake alaƙantawa da tsadar rayuwa da hauhawar farashin abubuwa.

Saboda Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka doga da shigo da kayyakin amfani irin su motoci da tufafi da sauran kayayyakin laturoni, kuma dole idan za a shiga da irin wadannan kayayyaki ana buƙatar chanjin kuɗin ƙasashen waje.

Yusha'u Aliyu ya ce matakin da gwamnati ta ɗauka na barin kudin ƙasar su nemo wa kansu daraja, ya taimaki wajen kawo hauhawar farashi a Najeriya.

"Yadda gwamnati ta bar wa masu musayar chanjin kuɗin ƙasar waje su yi chanjin kuɗin yadda suka ga dama, wata babbar matsala ce da ta haddasa ƙaruwar farashin'', in ji shi.

Popular posts from this blog

Matakan Da Gwamnatin Najeriya Ta Dauka Na Kayyade Farashi Ba Zai Kawar Da Yunwa Ba

Masana tattalin arziki a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin kasar ke dauka da kyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo karshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da bude iyakoki domin shigowa da abinci cikin kasar ba. ‘Yan Najeriya, musanman talakawa na ci gaba da kukan tsada da hauhawar kayan masarufi a kasuwannin kasar. Biyo bayan zanga zangar lumana da wasu mata suka jagoranta a jihar Neja da kuma wasu daban da aka gudanar a jihohin Kano da Osun, ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, daukan matakan ba da umarnin fito da tan-tan na abinci da ke runbunan gwamnantin kasar, domin karya farashin kayan masarufi da ke neman ya gagari kundila. To sai dai kuma a cewar wani masanin harkar gona, Farfesa Abubakar Gudigi, na jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, ya ce da sake a wannan dabara ta gwamnati. Gudigi ya ce matakin gwamnati na karya farashi, ba shi zai kawar da yunwa ba, domin yanzu haka akwai wadanda ke sayen kayan abinci a kauyuka, domin sayarwa...

Ko shigar da abinci Najeriya zai samar da mafita ga tsadar rayuwa?

A ke ciki sannan dan kasuwa shi ma yana fuskantar koma-bayan ciniki saboda mutane na fama wajen samun kudin da za su shiga kasuwa. Ya ce tsugunu ba ta kare ba a damar da gwamnati ta bayar na ba da dala ga duk mai son shigar da abinci daga wasu kasashen kasancewar dalar ta yi karanci a babban bankin Najeriya. "Domin duk wanda zai siyo abinci a waje, ko dai ya canza naira zuwa dala, ko naira zuwa CFA, ko zuwa me ka canza naira, idan ka siyo abincin ba za ka sayar da shi a kan sauki ba." in ji Dr Kani. Dr Muhammad Suleiman Kani ya ce matukar gwamnati na son kawo sauki toh kamata ya yi gwamnati ta haramta shigar da duk kayan da za a iya samu a Najeriya. A cewarsa, idan gwamnati ta dauki wannan mataki, ya kamata ta hanzarta tayar da komadar kamfanoni da wutar lantarki domin su tsaya da kafafunsu. Ya kuma yi kira ga shugaban kasa ya tashi tsaye wajen yin abin da ya dace domin fitar da Najeriya daga kangin da take ciki. A cewar masanin, ya kamata gwamnati ta cika alkawur...

Kuskuren Farko da Tinubu Yayi Ya Jefa Mutanen Najeriya a Wahala.

Tsohon shugaban PACAC, Itse Sagay ya soki gaggawan janye tallafin man fetur da aka yi a bara Farfesan yana gani kyau sabon shugaban Najeriya ya jira sai matatun cikin gida sun fara aiki tukun Itse Sagay yana sa ran gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kawo sauyin al’amura a Najeriya  - Itse Sagay Farfesa ne kuma babban lauya a Najeriya, ya soki tsarin janye tallafin man fetur da aka tabbatar da shi a 2023. A wata zantawa da tashar Channels tayi da shi, Farfesa Itse Sagay ya yi tir da da Bola Tinubu a kan daina biyan tallafin man fetur.  Itse Sagay ya bada misali da matatar Aliko Dangote da ta gwamnati da ke Fatakwal, ya so ina ma sun fara aiki kafin fetur ya tashi. Itse Sagay bai ji dadin tashin fetur ba "Fetur yana da muhimmanci a rayuwarmu.  Tsadar rayuwa ta na ta karuwa kuma rayuwa tayi kunci. Ina tunani ya kamata a ce mun jira na watanni shida domin za a fara tace mai a gida, sai a cire tallafi. Gaggawa da yadda aka janye tallafin nan ta ke ya kirkiro wahalar...