Tsohon shugaban PACAC, Itse Sagay ya soki gaggawan janye tallafin man fetur da aka yi a bara Farfesan yana gani kyau sabon shugaban Najeriya ya jira sai matatun cikin gida sun fara aiki tukun Itse Sagay yana sa ran gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kawo sauyin al’amura a Najeriya
- Itse Sagay Farfesa ne kuma babban lauya a Najeriya, ya soki tsarin janye tallafin man fetur da aka tabbatar da shi a 2023. A wata zantawa da tashar Channels tayi da shi, Farfesa Itse Sagay ya yi tir da da Bola Tinubu a kan daina biyan tallafin man fetur.
Itse Sagay ya bada misali da matatar Aliko Dangote da ta gwamnati da ke Fatakwal, ya so ina ma sun fara aiki kafin fetur ya tashi. Itse Sagay bai ji dadin tashin fetur ba "Fetur yana da muhimmanci a rayuwarmu.
Tsadar rayuwa ta na ta karuwa kuma rayuwa tayi kunci. Ina tunani ya kamata a ce mun jira na watanni shida domin za a fara tace mai a gida, sai a cire tallafi. Gaggawa da yadda aka janye tallafin nan ta ke ya kirkiro wahalar da kusan da kyar ake rayuwa.
Daily Trust ta ce Sagay bai goyon bayan yadda ake tafiyar da abubuwa a yau, ya sha bam-bam da gwamnatin da aka rantsar a bara.
Dole Shugaba Tinubu ya ceci Naira
A hirar da aka yi da shi, lauyan ya ce dole sai an yi hobbasa domin a ceci Naira wanda kullum ta ke kara rasa daraja a kan Dala. Ko a mafarki, Farfesan bai taba tunanin za a zo lokacin da za a canji Dalar Amurka a kan N1, 000, sai dai yana sa ran za a kawo gyara.
Gwamnatin Tinubu ta jawo tsadar fetur
A dalilin janye tallafi da gwamnati tayi, ana da labarin farashin litar man fetur ya tashi daga N190 zuwa kusan N700 a fadin kasar. Kwanaki an yi ta rade-radin fetur zai kara kudi, zancen da gwamnati ta karyata, ta kuma nuna ba a dawo da biyan tallafin man ba.
AMH HAUSA