Skip to main content

Matakan Da Gwamnatin Najeriya Ta Dauka Na Kayyade Farashi Ba Zai Kawar Da Yunwa Ba


Masana tattalin arziki a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin kasar ke dauka da kyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo karshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da bude iyakoki domin shigowa da abinci cikin kasar ba.

‘Yan Najeriya, musanman talakawa na ci gaba da kukan tsada da hauhawar kayan masarufi a kasuwannin kasar.

Biyo bayan zanga zangar lumana da wasu mata suka jagoranta a jihar Neja da kuma wasu daban da aka gudanar a jihohin Kano da Osun, ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, daukan matakan ba da umarnin fito da tan-tan na abinci da ke runbunan gwamnantin kasar, domin karya farashin kayan masarufi da ke neman ya gagari kundila.

To sai dai kuma a cewar wani masanin harkar gona, Farfesa Abubakar Gudigi, na jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, ya ce da sake a wannan dabara ta gwamnati.

Gudigi ya ce matakin gwamnati na karya farashi, ba shi zai kawar da yunwa ba, domin yanzu haka akwai wadanda ke sayen kayan abinci a kauyuka, domin sayarwa da tsada, haka kuma dole a karya farashin kayan masarufi da dawo da darajar Naira.

Ko a makon da ya gabata sai da wata kotun tarayya da ke jihar Legas ta umarci gwamnatin Najeriya da ta dauki kwararan matakai na kawo karshen hauhawar kayan masrufi na kafa hukumar kaiyade farashin abinci ta kasa.

Wasu ‘yan Najeriya sun cewa akwai bukatar gwamnati ta dauki mataki na dawo da darajar Naira da bunkasa noma da tattalin arziki dama dawo da tallafin man fetur.

A bangarensa dai Farfesan harkar Noma Abubakar Gudigi cewa ya yi akwai matakin da gwamnati ya kamata ta dauka na hana manyan ‘yan kasuwa shiga kauyuka domin saye kayan gona daga manoma.

Yanzu dai a yayin da gwamnati ta dauki matakai na rage farashin kayan abinci, abun jira a gani shi ne ko matakan zasu taimaka wajen kawo sauki ga ‘yan kasa.

AMH HAUSA 

Popular posts from this blog

Wato tazarar da'awar Dr. DT ta matuqar shan banban da ta Sheikh Albani (Ra) musamman a wannan datsin, wayewar su da mu'amala ba daya bane.

Yanzu nake ganin wata sanarwa ta neman shi ido rufe daga ofishin shugaban yan sanda na Bauchi da Gomnatin ta. Naji ba dadi ganin hakan in gaskiya ne, kuma abin takaici ne, sai dai da yawa almajirai suke janyo irin matsalar nan da mashawarta. Sheikh Albani yayi rikici da Gomnati sosai a lokacin sa, kuma shine yake nasara, duba da yasan Shari'a, yasan doka dai dai gwargwado, ga wayewa ga bin abubuwa sannu a hankali wajen mu'amalantar wanda suka saba dashi bakin iyawan shi, musamman a karshe karshen da'awar shi a duniya. Abin burgewa daliban da Sheikh Albani ya gamsu dasu a matsayin dalibai da abokai, basa yin hargowa a komai domin wayewar su da kuma tarbiyyar da ya masu. Amma shi DT matsalar rikicinsa da kowa da rushe duk abinda gomnati ya yarda dasu a matsayin dai dai kun mutane da kuma Kungiyoyi da Jagorori, wanda Sheikh Albani har Jam'iyya yana da ita ba iya Kungiya ba, ko a iya baki ne duk wadanda ya jinginu dasu zasu ji dadi kuma in abu ya taso zasu tsayu...

Jihohin arewacin Najeriya bakwai da za su fuskanci yunwa

-Bankin Duniya A wani rahoto da bankin na duniya ya wallafa tun ranar 1 ga watan Fabrairu kuma ya samu watsuwa a ranar 8 ga watan na Fabrairu ya fitar da bayan na sassan duniya da matsalolin yunwa da za su fuskanta. A sashen Afirka ta yamma da ta tsakiya, rahoton mai taken 'Food Security Update 2024', ya bayyana cewa wasu jihohi guda bakwai na arewa maso yammaci da gabashi da wadanda za su fuskanci matsalar yunwa tun daga farkon shekarar nan har zuwa watan Mayu. Jihohin dai su ne: Adamawa Borno Kaduna Katsina Sokoto Yobe Zamfara. Rahoton dai ya bayyana dalilan rashin tsaro na 'yan bindiga da ke satar jama'a a jihohi kamar Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara, inda su kuma Borno da Yobe da Adamawa ke fuskantar matsalar Boko Haram. Harwayau, rahoton ya yi wa jihohin kudin goro da sauran sassan Najeriya da ke fama da matsalar tsadar rayuwa a matsayin daya daga cikin dalilan da zai sa jihohin su fuskanci yunwa. Da ma dai bankin na duniya a wani rahoto ya ayyan...

Yunwa da Zanga-zanga: Ka maido da shirin NSIPA a fadin kasar

Adeyanju ya ce zanga-zangar da aka yi a jihohin Neja, Kano, da Kogi sun nuna irin girman halin Ana tsaka da wahalhalun da ke addabar Najeriya, Deji Adeyanju, wani fitaccen mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba batun dakatar da shirin zuba jari na kasa. Adeyanju ya ce zanga-zangar da aka yi a jihohin Neja, Kano, da Kogi sun nuna irin girman halin da ‘yan Najeriya ke ciki da kuma bukatar Tinubu ya dauki kwakkwaran mataki. Ku tuna cewa Tinubu ya dakatar da duk wasu shirye-shiryen da Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA) ke gudanarwa a kan zargin damfarar kudi da babbar jami’ar zartarwa Halima Shehu ta yi. Sai dai Adeyanju ya yi gargadin cewa ci gaba da dakatar da wadannan shirye-shiryen na da illa ga ‘yan Najeriya. A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Adeyanju ya ce: “Yayin da muka amince da dakatar da duk wasu shirye-shiryen da Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA) ta gudanar a wani bangare na binciken da ake yi kan zar...