Wato tazarar da'awar Dr. DT ta matuqar shan banban da ta Sheikh Albani (Ra) musamman a wannan datsin, wayewar su da mu'amala ba daya bane.
Yanzu nake ganin wata sanarwa ta neman shi ido rufe daga ofishin shugaban yan sanda na Bauchi da Gomnatin ta.
Naji ba dadi ganin hakan in gaskiya ne, kuma abin takaici ne, sai dai da yawa almajirai suke janyo irin matsalar nan da mashawarta.
Sheikh Albani yayi rikici da Gomnati sosai a lokacin sa, kuma shine yake nasara, duba da yasan Shari'a, yasan doka dai dai gwargwado, ga wayewa ga bin abubuwa sannu a hankali wajen mu'amalantar wanda suka saba dashi bakin iyawan shi, musamman a karshe karshen da'awar shi a duniya.
Abin burgewa daliban da Sheikh Albani ya gamsu dasu a matsayin dalibai da abokai, basa yin hargowa a komai domin wayewar su da kuma tarbiyyar da ya masu.
Amma shi DT matsalar rikicinsa da kowa da rushe duk abinda gomnati ya yarda dasu a matsayin dai dai kun mutane da kuma Kungiyoyi da Jagorori, wanda Sheikh Albani har Jam'iyya yana da ita ba iya Kungiya ba, ko a iya baki ne duk wadanda ya jinginu dasu zasu ji dadi kuma in abu ya taso zasu tsayu akan lamarin.
Shi kuma DT ba ruwan shi da kowa, musamman dattijai da masu hankalin gaban shi, sai wasu yara da yan media da masu bashi gurguwar shawara yake bi, tsakani ga Allah bama jin dadin rikicin malamai da malamai, balle muga yan siyasa zasu ci zarafin mai addini koda mun saba a manhaji da matsotsar addini.
Koma dai menene fatan mu Allah ya gyatta lamuran mu dashi ya bamu mafita dashi da sauran yan uwa ya shiryar damu ya tsaremu daga afkawa cikin mummunan kaddara don tsarkin sunayen ka.