Skip to main content

Jihohin arewacin Najeriya bakwai da za su fuskanci yunwa

-Bankin Duniya

A wani rahoto da bankin na duniya ya wallafa tun ranar 1 ga watan Fabrairu kuma ya samu watsuwa a ranar 8 ga watan na Fabrairu ya fitar da bayan na sassan duniya da matsalolin yunwa da za su fuskanta.

A sashen Afirka ta yamma da ta tsakiya, rahoton mai taken 'Food Security Update 2024', ya bayyana cewa wasu jihohi guda bakwai na arewa maso yammaci da gabashi da wadanda za su fuskanci matsalar yunwa tun daga farkon shekarar nan har zuwa watan Mayu.
Jihohin dai su ne:
Adamawa
Borno
Kaduna
Katsina
Sokoto
Yobe
Zamfara.
Rahoton dai ya bayyana dalilan rashin tsaro na 'yan bindiga da ke satar jama'a a jihohi kamar Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara, inda su kuma Borno da Yobe da Adamawa ke fuskantar matsalar Boko Haram.

Harwayau, rahoton ya yi wa jihohin kudin goro da sauran sassan Najeriya da ke fama da matsalar tsadar rayuwa a matsayin daya daga cikin dalilan da zai sa jihohin su fuskanci yunwa.
Da ma dai bankin na duniya a wani rahoto ya ayyana Najeriya a matsayin kasa ta 6 a jerin kasashen da suka fi talauci har Mutane na shan ruwan zafi saboda yunwa a Najeriya'

Wadanne matakai za a bi domin rage radadin yunwa?

Masana na cewa matakan iri biyu ne wato na gajere da dogon zango:

Gajeren zango:

Dr Mohammed Sulaiman Kani masani kan tattalin arziki da samar da abinci kuma malami a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Kano ya ce dole ne gwamnonin jihohin da abin ya shafa su bude rumbunan abinci na jihar su fito da kayan abinci a sayar a kan farashi mai rahusa.

Masanin ya kara da cewa "dole ne a yi kokarin samar da kwarkwaryar tsaro ga mutanen yankunan domin samun damar yin noma."
Dogon zango:

Dangane kuma da matakai na dogon zango, masanin ya lissafa abubuwa guda hudu:
Tsaro
Noma
Samar da wutar lantarki
Tabbatar kamfanonin cikin gida sun tashi
"Idan dai har gwamnati ba za ta tabbatar da wadannan abubuwan ba to fa a rahoton bankin na duniya na nan gaba za a iya ganin sunayen wasu jihohin sabbi sun fado cikin yanayin yunwa da talauci,"

 in ji Dr Mohammed Kani.

AMH Hausa 

Popular posts from this blog

Wato tazarar da'awar Dr. DT ta matuqar shan banban da ta Sheikh Albani (Ra) musamman a wannan datsin, wayewar su da mu'amala ba daya bane.

Yanzu nake ganin wata sanarwa ta neman shi ido rufe daga ofishin shugaban yan sanda na Bauchi da Gomnatin ta. Naji ba dadi ganin hakan in gaskiya ne, kuma abin takaici ne, sai dai da yawa almajirai suke janyo irin matsalar nan da mashawarta. Sheikh Albani yayi rikici da Gomnati sosai a lokacin sa, kuma shine yake nasara, duba da yasan Shari'a, yasan doka dai dai gwargwado, ga wayewa ga bin abubuwa sannu a hankali wajen mu'amalantar wanda suka saba dashi bakin iyawan shi, musamman a karshe karshen da'awar shi a duniya. Abin burgewa daliban da Sheikh Albani ya gamsu dasu a matsayin dalibai da abokai, basa yin hargowa a komai domin wayewar su da kuma tarbiyyar da ya masu. Amma shi DT matsalar rikicinsa da kowa da rushe duk abinda gomnati ya yarda dasu a matsayin dai dai kun mutane da kuma Kungiyoyi da Jagorori, wanda Sheikh Albani har Jam'iyya yana da ita ba iya Kungiya ba, ko a iya baki ne duk wadanda ya jinginu dasu zasu ji dadi kuma in abu ya taso zasu tsayu...

Yunwa da Zanga-zanga: Ka maido da shirin NSIPA a fadin kasar

Adeyanju ya ce zanga-zangar da aka yi a jihohin Neja, Kano, da Kogi sun nuna irin girman halin Ana tsaka da wahalhalun da ke addabar Najeriya, Deji Adeyanju, wani fitaccen mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba batun dakatar da shirin zuba jari na kasa. Adeyanju ya ce zanga-zangar da aka yi a jihohin Neja, Kano, da Kogi sun nuna irin girman halin da ‘yan Najeriya ke ciki da kuma bukatar Tinubu ya dauki kwakkwaran mataki. Ku tuna cewa Tinubu ya dakatar da duk wasu shirye-shiryen da Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA) ke gudanarwa a kan zargin damfarar kudi da babbar jami’ar zartarwa Halima Shehu ta yi. Sai dai Adeyanju ya yi gargadin cewa ci gaba da dakatar da wadannan shirye-shiryen na da illa ga ‘yan Najeriya. A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Adeyanju ya ce: “Yayin da muka amince da dakatar da duk wasu shirye-shiryen da Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA) ta gudanar a wani bangare na binciken da ake yi kan zar...